ABNA24 : Majiyar muryar Jumhuriyar Musulunci Iran ta nakalto majiyar rundunar tana fadar haka a jiya Laraba, ta kuma kara da cewa tuni wata kotu a kasar ta fidda sammacin kama wanda aka kaman, sai dai rundunar ba ta bayyana sunan wanda aka Kaman ba.
Dakarun Hashdushabi dai sune suka jagoranci yaki da kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh wacce ta mamaye arewacin kasar daga shekara ta 2014 -2017.
Duk da cewa an kawo karshen ikon kungiyar ‘yan ta’addan a kasar ta Iraki, amma har yanzun akwai daddaikun mayakansu aboye a duk fadin kasar.
A cikin yan watannin da suka gabata ne dakarun na Hashd suka fara aikin kakkabo ragowar ‘ya’yan wannan kungiyar a lardunan Salahuddeen, Ambar da kuma Diyalah.
342/